Badakalar 4bn: EFCC ta mikawa yan fansho na jihar Kano gidaje 324

0
228

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC ta miƙa wa wasu ƴan fansho na jihar Kano takardun gidajensu 324 da aka ƙwato.

An miƙa wa ƴan fanshon gidajen ne bayan umarnin ƙwace su a karo na ƙarshe da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar.

Sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X a yau Talata ta ce umarnin kotun da Mai Shari’a I.E. Ekwo ya bayar, ya biyo bayan nasarar binciken da ta gudanar ne kan wani asusu na Naira biliyan 4.1 da ‘yan fanshon suka bayar don mallakar gidaje, “inda aka yi sama da faɗi da kuɗaɗen a lokacin gwamnatoci biyu da suka wuce na jihar Kano.”

EFCC ta yi binciken ne bayan wani ƙorafi da wata ƙungiya ta ƴan fanshon jihar Kano ta shigar mata, kan zargin yin almundahana da kuɗaɗen fansho a jihar.

“Wani bincike da hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa gwamnatin jihar ta ƙulla yarjejeniya da asusun fansho na jihar Kano ta gina gidaje a kan jimillar kuɗi naira biliyan 41, wanda asusun fanshon ne zai ba da naira biliyan huɗu da miliyan 100 daga cikin kuɗin,” a cewar sanarwar ta EFCC.

EFCC ta ƙara da cewa sai dai kuma an yi amfani da gudunmawar ’yan fanshon wajen gina gidajen a wasu rukunun gidaje guda uku na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo City da Sheikh Nasiru Kabara (Amana) City da kuma Sheikh Khalifa Ishaq Rabi’u City, duk a jihar Kano.

“An gano cewa tsofaffin gwamnoni biyu na jihar sun yi almundahana ta hanyar yin sayar da gidajen ga ‘yan’uwa da abokan arzikinsu a farashi mai rahusa, aka bar ma’aikatan fansho da rashin isasshen kudi a asusunsu da kuma gidajen da ba a kammala su ba.

“Shigar EFCC cikin lamarin ne ya sa aka kammala bincike aka shigar da ƙara tare da samun nasarar ƙwato gidaje 324 aka miƙa wa hukumar fansho ta Jihar Kanon,” in ji hukumar.

Yayin da yake miƙa takardun kadarorin 324 na Naira biliyan 4.1 ga ‘yan fansho a ranar Litinin 18 ga Maris, 2024, Kwamandan Hukumar EFCC na shiyyar Abuja, Adeniyi Adebayo ya tabbatar da cewa EFCC za ta ci gaba da ƙoƙarin kawar da ayyukan damfara.

Wakilan Hukumar Fansho ta Jihar Kano, Alhaji Hassan Muhammed Aminu da Kubra Ahmad Bichi da Salisu Yakubu Abubakar, wadanda suka karbi takardun a madadin ma’aikata da ‘yan fansho, sun bayyana jin dadinsu kan taimakon da EFCC ta musu wajen ƙwato gidajensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here