Majalisar Dattawan Najeriya za ta gayyaci tsohon gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele domin amsa wasu tambayoyi dangane da bashin naira tiriliyan 30 da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta karɓa.
Majalisar dai za ta buƙaci Emefiele ya yi mata bayani a kan wani bashin Naira tiriliyan 30 da ya bai wa Gwamnatin Tarayya a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban kwamitin kula da huldar kuɗi tsakanin gwamnatin tarayya da CBN, Sanata Jibrin Isah ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan zaman kwamitin da wakilan CBN a ranar Talata.
Isa ya ce alamu na nuna cewa Emefiele ya zartar da waɗansu hukunce-hukunce da a ka’ida bai kamata ya yi su kai tsaye ba, sai ya tuntubi mambobin kwamitinsa, mataimakinsa da kuma masu ruwa da tsaki a lamarin.
Tuni dai majalisar ta kaddamar da wani kwarya-kwaryan kwamiti na musamman domin binciken yadda aka bada bashin da yadda aka kashe kudin da aka ranta.
Haka zalika, kwamitin da Sanata Jibrin Isah zai jagoranta zai binciki yadda aka bayar da bashi nan na Anchor Borrowers a zamanin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Sanata Jibrin Isa ya ce, “mun dubi kundin ancho borrowers da na waya and means a gaban zauren Majalisar Dattawa, mun ga abubbuwa da yawa a cikinsa, mun dubi wadanda suka amfana da basukan.
Wannan zai taimaka mana gano gaskiyar abin da ya wakana a CBN zamanin Emefiele.
“Babban abin da ya sa kila dole mu gayyaci tsohon gwamnan bankin shi ne wakilan CBN din da suka zo sun gaza amsa tambayoyin da mu ka yi musu, wanna shi ne zai tabbatar da cewa ba su da cikakken sanin abubuwan da suka wakana dangane da waɗannan kudi da aka rantawa gwamnatin tarayya.”
Bayanai sun ce wakilan CBN a gaban kwamitin dai sun gaza amsa tambayoyin da kwamitin majalisar dattawan ya yi gare su ne, sun bukaci a basu dama su je su binciko su dawo.
Sanata isa yace “lallai idan shugabannin bankin na wannan lokacin suka gaza kawo mana bayanan da muke bukata, to ya zama wajibi mu gayyaci Emefielle ya gurfana a gabanmu domin faɗa mana yadda aka yi.”
Dangane da bashin manoma na Anchor Borrowers kuwa, Isa cewa ya yi, “kawo yanzu an dawo da kaso 70, sauran kaso 30 ɗin na wurin kananan manoma.
Babban hatsarin da ke tattare da bai wa kananan manoma bashi, shi ne gaskiya ba su da wata dama ta kere sa’a, ko kuma kaiwa ga tudun mun tsira, sakamakon yadda abubbuwa suke”.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa “kananan manoma ba su da kwarewar aikin noma na zamani, kuma ba su da kayan aiki, wannan matsala ce da idan aka yi wasa za ta hana mu samun abin da muke so.
Kwamitin majalisar ya bayyana cewa kuɗin da ke hannun ƙananan manoma yakai Naira Biliyan 358, amma inda ake sa ran samun sauki shine, an raba wannan rance ne ta hannun bankunan yan kasuwa, dan haka yanzu su za su san yadda za su yi su karbo kudin gwamnati.
CBN dai ya bai wa Gwamnatin Buhari rancen kuɗi kan tsaron da ake yi wa lakabi da “ways and means” a turance domin cike gibin kasafin kudi.
Ana iya tuna cewa, tsohuwar gwamnatin ta karbi rancen kuɗin ne domin samun damar aiwatar da wasu muhimman ayyuka ba tare da fita ketare karbo bashi ba.