Mata 4 sun mutu a wajen karbar zakka a Bauchi

0
161

Rundunar ƴansadan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mata gudu huɗu a wurin turmurtsutsun bayar da zakka a jihar.

Turmutsutsun ya faru ne a safiyar yau Lahadi a cibiyar Shafa Holding Company kan hanyar Jos da ke jihar.

Mai magana da yawun ƴansandan jihar, Ahmed Wakili ya tabbatar wa da BBC cewa bayan faruwar lamarin ne, jami’ansu suka garzaya wurin domin kwashe mutanen da abin ya shafa.

“Cikin matan akwai wata matashiya mai shekara 17 Na’ima Abdullahi mazauniyar garin Bauchi, ita kaɗai ta rage a raye,” in ji shi.

Ya yi kira ga masu hannu da shuni da cewa su rika sanar da ƴansanda idan za su yi irin wannan aiki na bayar da zakka don su taimaka wajen shawo kan dandazon mutane.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, yayin da ake ci gaba da bincike don gano abin da ya haddasa lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here