Muna samun nasara a yaki da masu aikata laifuka – Sojin Najeriya

0
161

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana samun nasara a yakin da take da masu ta da ƙayar baya da sauran masu aikata manyan laifuka a ƙasar.

Wannan na ƙunshe ne cikin jawabin da daraktan watsa labarai na hedikwatar Edward Buba ya yi wa manema labarai a jiya a Abuja babban birnin kasar.

Da yake yi wa BBC ƙarin bayani Group Captain Ibrahim Ali Bukar ya ce a kowanne mako suna tattauara bayanai kan nasara da ci gaba da aka samu a ƙasar nan.

Ya ce “haƙiƙanin gaskiya an samu nasara tukuru, mun kama yaran da suke garkuwa da mutane, kuma an kwato wadanda aka yi garkuwa da su da dama, kuma an sake hada su da iyayensu.

“A Kudu maso Kudancn Najeriya, inda ake samun matsalar sacewa ƙasar nan mai, an lalata ramatattun matatun mai da ake amfani da su a yankin 51, idan za a ƙiyasta abin a kuɗi zai kai wurin naira biliyan ɗaya,” in ji shi.

Ya ce dakarun Najeriya sun kwato manyan makamai na zamami kusan 171, an kwato harsasai kimanin 2252.

A dai yankin na Naija Dalta an kwato jirgin ruwa da suke amfani da su kusan 17.

Ya kuma ce anan ana neman wadanda suka kashe sojojin Najeriya 18 a jihar Naija ruwa a jallo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here