‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda a jihar Imo

0
153

Wasu ‘yan bindiga da ake zargi mambobin ƙungiyar IPOB ne sun kashe wasu ‘yan sanda biyu da ake aikin sintiri a jihar Imo.

Jami’an waɗanda rundunar Mopol ta 18, an musu kofar rago ne a safiyar ranar Asabar yayin da suke aiki a kan titin Gariki, an jefa musu wani abin fashewa ne a motarsu dadlin da ya sanya suka fara musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar.

Rahotanni sun ce garin haka ne waɗan nan jami’ai suka rasu, hudu kuma suka tsira daga harin.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Aboki Danjuma ya yi tir da wannan hari da ya yi ajalin jami’an.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here