Gwamnati Najeriya ta maka kamfanin Binance a kotu 

0
174

Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙara kan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar tara haraji ta Najeriya, FIRS ce ta sanar da matakin, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin na Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaƙa da ƙin biyan haraji.

Cikin waɗanda ake ƙarar akwai Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, dukkansu manyan shugabannin Binance da yanzu haka ke tsare a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Binance sun haɗa da zargin ƙin biyan harajin VAT kan kayayyakin more rayuwa da harajin da kamfanoni ke biya na kuɗin shigar da suke samu da ƙin biyan kuɗaɗen harajin da suka karɓa da kuma haɗa baki da abokanan hulɗarsu wajen kaucewa biyan haraji ta shafinta.

A cewar gidan Talabijin na Channels, gwamnatin Najeriya tana zargin Binance da ƙin yin rajista da hukumar FIRS saboda dalilai na haraji da kuma saɓawa dokokin biyan haraji a ƙasar.

Ɗaya daga cikin tuhumar da ake yi ta shafi gazawar Binance na karɓa da kuma biyan nau’ikan haraji ga gwamnati kamar yadda yake a sashe na 40 na dokar FIRS ta 2007 da aka yi wa gyaran fuska.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan ƙudurinta na tabbatar da cewa kamfanonin kirifto suna mutunta dokokinta na haraji tare da magance almundahana a tsakanin irin kamfanonin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here