Kotu ta hana Murja Kunya amfani da dandalin sada zumunta 

0
194
Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Wata babbar kotu da ke Kano ta ba da belin fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya a kan kuɗi naira dubu 500 da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata.

Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun kotunan Kano ya tabbatar wa BBC wannan labarin, inda ya ce kotun ta ba da belin Murja ne bayan zaman kotun da aka yi a yau Litinin.

Alƙalin ya ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya mata ya zama ɗan’uwanta na jini, sannan ɗayan kuma dole ne ya zama yana da shaidar mallakar fili a Kano.

Alƙali Nasiru Saminu ya kuma ce ya bayar da belinta ne bisa hujjar cewa matashiyar ‘yar Tiktok din ta wuce kwana 30 a garƙame.

Sai dai alƙalin ya haramta wa jarumar tiktok ɗin amfani da shafukan sada zumunta har zuwa lokacin kammala shari’ar.

Alƙalin ya kuma ce kwamishinan ƴansanda na da ikon sake kama Murja matuƙar ta ƙi mutunta umarnin haramta mata amfani da shafukan sada zumuntar tare da gabatar da ita gaban kotu.

Mai shari’ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Mayu don ci gaba da zama.

Hukumar Hisba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami’an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi yada baɗala a shafukan sada zumunta.

Daga bisani kuma wata kotu a Kano ta tura ƴar tiktok ɗin zuwa asibitin kula da lafiyar masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here