NAHCON ta kara kudin kujerar Aikin Hajjin bana

0
193

Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta ƙara farashin kujerar Aikin Hajjin bana da miliyan N1,918,032.91, inda ta bai wa maniyyata wa’adin zuwa 28 ga watan Maris ɗin 2024 su biya cikon kuɗin. 

Mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi. 

Hukumar ta NAHCON ta ce an samu wannan ƙarin ne sakamakon ƙaruwar farashin dala a Nijeriya. 

A baya dai NAHCON ta saka kuɗin Aikin Hajjin bana kan Naira miliyan 4.9, lamarin da ya sa aka yi ta kokawa da hakan. 

Sai dai a halin yanzu ana buƙatar waɗanda suka biya kafin alƙalamin na miliyan 4.9 su biya ƙarin miliyan 1.9, wanda hakan ya kai jumullar kuɗin kowane maniyyaci zuwa miliyan 6.8. 

Haka kuma hukumar ta bai wa maniyyatan zuwa 28 ga watan Maris su biya wannan cikon. 

Sai dai a wani ɓangaren kuma hukumar ta sanar da cewa duk wani sabon maniyyaci daga arewacin Nijeriya wanda yake son biyan kuɗin kujera a yanzu zai biya N8, 254, 464.74.

Sai kuma sabbin maniyyata daga jihohin Adamawa da Borno za su biya  N8,225, 464.74 sai kuma ƴan kudancin Nijeriya za su biya N8, 454, 464.74.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here