Ƙarin kudin hajji bai shafi masu adashin gata ba – NAHCON

0
213
Hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa ƙarin kuɗin kujerar hajj da ta yi a baya-bayan nan ba zai shafi maniyyatan da suka biya ta tsarin adashin gata ba.

Hukumar ta Nahcon ta bayyana haka ne ƴan kwanaki bayan fitar da sabon farashin kujerar hajjin ga maniyyatan bana.

Nahcon ta ce ita ce za ta ɗauki nauyin biyan cikon kuɗaɗen maniyyatan da suka biya ta tsarin adashin gata abin da ke nufin maniyyatan ba za su biya ƙarin ko sisi ba.

A ranar Lahadi ne hukumar ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya tare da bai wa maniyyatan wa’adin kwana huɗu su cika kuɗin.

Ta jingina matakin nata ga yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa wadda da ita ce ake yin ƙiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke buƙata.

Tun bayan sanar da ƙarin kuɗin ne al’umma suke ta bayyana ra’ayoyinsu inda wasu ke ganin matakin ya zo a ƙurarren lokaci ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa a ƙasar.

Adashin gata tsari ne da Nahcon ya ɓullo da shi shekarun da suka gabata domin saukakawa maniyyata wajen tara kudin gwargwadon halin da mutum yake da shi.

Hukumar alhazai ta dauko wannan tsari na adashin gata daga kasashe kamar Malaysia da Indonesia, inda ‘yan kasar ke irin wannan tarin kudi don sauke faralli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here