Amurka ta amince ta janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar

0
183

Amurka ta ce ta amince za ta janye sojojinta da suke cikin jamhuriyar Nijar baki-ɗaya.

Hakan na zuwa ne yayin wata ganawa da aka yi tsakanin Jakadiya Amurka a Nijar Kathleen FitzGibbon da Ministan cikin gidan kasar Janar Tambo Muhamed kan sanarwar da sojojin Nijar suka fitar a ranar 16 ga watan Maris, wadda a cikin suka ce suna son yanke hulɗar soji tsakaninsu da Amurka.

Tun da fari sai da ofishin jakadancin Amurka ya nuna shakku kan matakin yana cewa bai samu wata sanarwa ba a hukumance ta neman sojojin su fice daga ƙasar.

Sai daga baya kuma sojojin suka aike wa ofishin takardar buƙatarsu a hukumance.

Hakan ya biyo bayan nuna rashin gamsuwa da halarcin yarjejeniyar sojin da Nijar take kallo a matsayin ƙarfaƙarfan da Amurka ta yi mata.

Madam Kathleen FitzGibbon tace ta amnce da hukumomin Nijar kan wannan mataki, amma za su samar da wani daftari da za a tsara yadda za a kwashe sojojin a hukumance.

A wani mataki na daban, jami’ar diflomasiyyar Amurkan ta tabbatar da a niyar Amurka ta cigaba da kasancewa tare da Nijar a koda yaushe, ta hanyar tallafin ayyukan raya kasa da hukumar USAID ke bayarwa.

Akwai sojojin Amurka 1,100 a cikin Nijar wadanda suke ayyuka daban-daban, kuma dukannsu an girke su ne a arewacin ƙasar.

Amurka dai na sanya miliyoyin dala a bangaren tsaron Nijar a kowacce shekara, kuma a cikin irin wannan aiki ne ta gina wani katafaren sansanin soji wanda yanzu aka nemi ta fice daga cikinsa.

Tun da fari Nijar ta nemi sojojin Faransa su fice daga ƙasarta.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here