CBN ya yi wa bankuna karin jarin da za su mallaka

0
190

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kara adadin kuɗin da bankunan kasuwanci za su mallaka a matsayin jari zuwa Naira biliyan 500. 

CBN, ya ce dole ne kowane banki da ke hada-hada har a ƙasashen ƙetare ya kasance yana da jarin da bai gaza Naira biliyan 500 ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata takardar da daraktan sashen tsare-tsare da sanya ido kan ka’idojin kudi, Haruna Mustafa, ya sanya wa hannu.

CBN, ya bai wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi wa’adin watanni 24 domin cika wannan ka’ida.

Wannan wa’adi zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2024, zuwa watan 31 ga Maris, 2026.

Bankunan da hada-hadarsu iya Najeriya ta tsaya, na buƙatar mafi ƙarancin jari na Naira biliyan 200 domin cikar ka’idar da CBN ya gindaya.

Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa ya zama wajibi bankunan da ke aiki a yankunan kasar nan su zama suna da jarin da bai gaza Naira biliyan 50 ba.

Ya kuma bayyana cewa bankin da ke son ya rika aiki a fadin Najeriya ba tare da karbar kudin ruwa ba na bukatar jari na Naira biliyan 20.

Bankin da zai rika aiki a wani yanki guda na kasar nan, na bukatar jarin da bai gaza biliyan 10 ba.

An shafe shekara 19 rabon da a yi wa bankuna karin kudi game da jarinsu.

Sanarwar ta bai wa bankuna shawarar hadewa domin tabbatar da samun jari mai kauri da kyautata ayyuka ga abokan hulɗarsu.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here