Gwamna Uba Sani ya mika daliban Kuriga hannun iyayensu

0
146

Gwamnatin jihar Kaduna da ke ta ce da miƙa ɗaliban makarantar Kuriga da aka sace ga iyayensu.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya ce sai da aka tabbatar da lafiyar kwakwalwar yaran da kuma lafiyar jikinsu gabanin a miƙa su ga iyayensu sannan su koma makaranta.

Gwamna Uba Sani ya ce yaran da suka saba da shi suke ɗaukarsa tamkar mahaifi a gare su, sun yi alƙawarin amfani da wannan jarrabawa da suka fuskanta wajen mayar da hanakali da jajurcewa kan karatunsu da sun koma makaranta.

“Gidauniyar Uba Sani za ta ci gaba da kula da karatunsu daga nan har matakin gaba da sakandire,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kaduna za ta biya iyalan malamin makarantar Malam Abubakar diyyar naira miliyan 10 wanda ya mutu a lokacin da ake tsare da su sakamakon rashin lafiya.

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin sake gida makarantar Kuriga daga bangaren firaimare har sakandire tare da zagayeta da katanga, da kuma samar mata da cikakken tsaro domin yaran su koma su ci gaba da karatu.

A ranar shida ga watan Maris ne aka fara satar farko a watan nan, kuma an yi ne a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram sun sace a kalla ƴangudun hijira 200, yawancinsu mata da ƙananan yara a lokacin da suka shiga daji yin ice.

Duk da ƙaddamar da nemansu da sojoji suka yi, amma hakan ta gagara, babu wanda aka yi nasarar kuɓutarwa.

Washegari watau ranar bakwai ga watan dai na Maris, ƴanbindiga suka tasa ƙeyar ɗalibai kusan 300 daga makarantar firamare da sakandare a jihar Kaduna.

Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar cewa ɗalibai 28 daga cikin waɗanda ‘yan bindigar suka sace sun tsere daga hannunsu.

A ranar tara ga watan Maris, ƴanbindiga sun sace ɗalibai ƴan makarantar allo 17 a wata makaranta da ke jihar Sakkwato.

Amma an sako su a ranar 22 ga watan Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here