EFCC ta kama mutane 74 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a Ogun

0
157

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta kama mutum 74 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a jihar Ogun.

Wata sanarwa da EFCCn ta fitar a shafinta na X, ta ce ta kama mutanen ne a ranar Juma’a a a unguwar G.R.A Shagamu, bayan binciken sirri da suka gudanar wanda kuma ya fallasa miyagun ayyuka da suke aikatawa.

Ta ce ta kwato kayayyaki da dama a hannun mutanen waɗanda suka haɗa da motocin alfarma guda uku, kwamfutoci uku, wayoyin hannu 124, babura biyu da sauransu.

Hukumar ta ce za ta aika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here