Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano

0
185

Fiye da fursunoni 100 ciki har da waɗanda ke cin sarka kan laifin kisan kai a gidajen kaso na Jihar Kano na neman a yi musu afuwa.

Kwanturolan Gidan Yarin Kano, Mista Suleiman Inuwa ne ya bayyana hakan da cewa fursunonin sun miƙa buƙatar neman a yi musu aikin gafara.

Mista Inuwa ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin yi wa fursunoni afuwa karkashin jagorancin Hajiya Azumi Namadi Bebeji ya ziyarci Gidan Yarin da ke Janguza.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Gidajen Yarin Kano, Musbahu Kofar Nassarawa ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce daga cikin fursunonin da ke neman afuwar har da waɗanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da ke fama da ƙalubale na rashin lafiya da kuma dattawa waɗanda suka manyanta.

Da take martani, Hajiya Azumi ta ce gwamnati za ta duba lamarin fursunonin inda za ta yi la’akari da shaidar da ta tabbatar masu neman afuwar sun kasance mutanen kirki da kyawawan ɗabi’u a tsawon lokacin da suka shafe a ɗaure.

A cewarta, “zan gabatar da batun fursunonin a gaban mai girma Gwamnan Jihar Kano,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Hajiya Azumi ta kuma yaba wa fursunonin da suka haddace Al-Qur’ani da waɗanda suka samu kiredit 9 a jarrabawar NECO da ke neman gurbin karatu a Jami’ar karatu daga nesa ta kasa (NOUN).

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here