Masu zanga-zangar adawa da matakin da Isra’ila ke dauka kan Gaza sun kutsa kai babban dakin taron da shugaban Amurka Joe Biden ke gudanar da taro da tsaffin shugabannin kasar wato Barrack Obama da Bill Clinton, don kaddamar da gidauniyar tara dala miliyan 25 don daukar nauyin takarar Biden din a zaben kasar na badi.
Shugabannin uku na jagorantar taron na birnin New York gaban dubban magoya bayansu kafin wasu daga cikin masu zanga-zangar su kutsa cikin dakin taron tare da ihun nuna takaicinsu game da yadda Joe Biden ya ki daukar kwakkwaran mataki kan Isra’ila don ta tsagaita wuta a Gaza.
Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar na cikin dakin taro ke ihun cewa “ka ji kunya Joe Biden” “ka ji kunya.”
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun rika musayar yawu da tsohon shugaban kasar Barrack Obama wanda ke kokarin yi musu bayani, amma suka ki sauraren sa.
Ko a wajen dakin taron an gano daruruwan masu zanga-zangar da ke ci gaba da ihu tare da amfani da kalmomi marasa dadi kan shugabannin a wani bangare na yunkurin tilasta musu su dauki mataki cikin gaggawa.
Sai dai kuma ana ganin mafi yawan masu zanga-zangar magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump wanda ke sake takara a yanzu ne, la’akari da yadda suke shan alwashin kawar da Joe Biden da kuri’a sakamakon yakin na Isra’ila.