Tinubu zai halarci bikin rantsar da zababben shugaban Senegal

0
177

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kai ziyara ƙasar Senegal don halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaba Bassirou Diomaye Faye.

Tinubu zai bar Abuja ne a ranar da za a yi bikin rantsuwar wato Talata, bayan ya samu gayyata a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya, ta ce Tinubu zai koma gida ne a dai wannan rana da zarar an kammala bikin na birnin Dakar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here