An gano gawar wani babban jami’in dan sanda a jihar Oyo

0
180

An gano gawar wani jami’in ɗan sanda mai muƙamin mataimakin kwamishinan ƴan sanda Gbolahan Olugbemiyashe a gidansa da ke Ogbomosho a jihar Oyo.

A cewar jaridun Najeriya, Olugbemi, da ke rundunar ƴan sanda ta jihar Legas, ya je hutu ne domin bikin ista inda ya gamu da ajalinsa.

Babban jami’in ɗan sandan wanda aka yaba masa saboda rawar da ya taka a zanga-zangar EndSars da aka yi domin nuna adawa da cin zalin jami’an tsaro, ya mutu ne a wani yanayi mai matuƙar ɗaure kai.

Mutuwar jami’in ta jefa abokan aikinsa da ke aiki a sashen binciken manyan laifuka cikin alhini.

Rundunar ƴan sanda ta bakin mai magana da yawun sashen binciken manyan laifuka, ASP Aminat Mayegun ta ce za a yi bincike kan mutuwar tasa inda ta ce ba lalle bane a ce ya kashe kansa ne kamar yadda ake raɗe-raɗi.

Wata majiyar ƴan sanda ta ce za a gayyaci wasu domin su amsa tambayoyi game da lamarin. Cikinsu har da waɗanda suka fara ganin gawar tasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here