Za a rantsar da sabon shugaban kasar Senegal

0
205

A ranar Talatar nan ne, za a rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, inda zai fara mulki.

Mista Faye ya yi nasara da kashi 54 cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka jinkirta a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyyu masu mulki.

A ranar Juma’a ne Kotun Kolin kasar ta yammacin Afirka, ta tabbatar da Mista Faye a matsayin wanda ya ci zaben na ranar 24 ga watan Maris 2024.

Ana sa ran gudanar da bikin ne a cikin wani zauren taro da ke wajen babban birnin kasar ta Senegal, Dakar.

Amma za a watsa bikin kai tsaye ta tashar talabijin da kuma rediyo na kasar.

An tsaurara matakan tsaro a kewayen fadar shugaban kasar yayin da ake shirin bikin rantsuwar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO zai kasance cikin shugabanni kusan 15 da za su halarci bikin a yau Talata.

Sauyin shugabancin bai kasance na kai tsaye salin-alin ba, daga Shugaba Macky Sall mai barin-gado zuwa ga Shugaba mai jiran-gado ba, Diomaye Faye.

Kafin a kai ga zaben, kasar ta yi fama da tarzoma mummuna bayan da Shugaba Sall ya yi yunkurin jinkirta zaben.

A da ya kamata a yi shi ranar 25 ga watan Fabarairu amma ya dage shi zuwa watan Disamba, abin da Kotun Kolin kasar ta haramta.

Bugu da kari shugaban mai jiran-gado, ya shaki iskar ‘yanci ne daga kurkuku ‘yan kwana 10 kafin zaben, albarkacin afuwar gwamnati.

A jawabin da ya gabatar na nasarar da ya samu a cikin harshen Faransanci da kuma Wolof, Faye ya ce abin da zai ba fifiko a mulkin nasa shi ne, sasanta al’ummar kasa, da kokarin samar da saukin tsadar rayuwa da yaki da rashawa.

Ya kuma yi alkawarin wanzar da salon mulki na ‘yan gaba-da-gaba-dai, wato ra’ayin sauyi na dunkulalliyar Afirka, domin mayar da kasar kan turbar ‘yancin kasar da ya ce an cefanar a rahusa.

Haka kuma ana ganin zai nemi sauya kudin kasar daga CFA da kasar ke amfani da shi a yanzu.

Zai kuma yi kokarin mayar da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO.

Mutane da dama a kasar ta Senegal na daukar, Mista Faye, wanda zai kasance shugaba mafi karancin shekaru a Afirka, inda yake da shekara 44, a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata.

Hakan ya sa suke cike da burin zai fitar musu da kitse daga wuta, ya samar musu da sauyin da suke matukar bukata a kasar, mai yawan jama’a sama da miliyan 18.

Ana daukan kasar mafi zaman lafiya da cigaban dumukuradiyya a Afirka, kasancewar tun da ta samu mulkin kai daga Faransa a ranar 4 ga watan Afirilu, na 1960 ba ta taba fadawa hannun mulkin soji ba.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here