An ci tarar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja naira miliyan 200

0
191

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta ɗauki matakin ladabtarwa kan kamfanin rarraba lantarki na Abuja, Aedc saboda rashin mutunta dokar ƙara kuɗin wuta.

Hukumar ta ci kamfanin tarar naira miliyan 200 saboda yadda kamfanin ya chaji wasu abokan hulɗarsa da matakin ƙarin bai shafa ba.

Matakin ya zo ne bayan ƙoken da abokan hulɗar kamfanin suka yi inda aka gano Aedc ya yi ƙarin kuɗin ne ga dukkan abokan hulɗarsa da ke kowane mataki saɓanin dokar ƙarin kuɗin da aka tsara ta domin tabbatar da adalci.

Nerc ta ce dole ne Aedc ya mayar wa kwastamominsa da ke aji na biyu zuwa ƙasa kuɗaɗensu musamman waɗanda aka yi wa ƙarin kuɗin da bai shafe su ba.

Sannan kuma kamfanin zai biya tarar ta nara miliyan 200 saboda saɓa dokokin hukumar.

Sanarwar da Nerc ta wallafa a shafinta na Tuwita ya nemi kamfanin na Aedc da ya gabatar wa hukumar shaidar mutunta umarnin da ta ba shi nan da 12 ga watan Afrilu.

Nerc ta ce ta ɗauki matakin ne domin cika alƙawarin kare haƙƙoƙin abokan hulɗa da tabbatar da adalci a ɓangaren wutar lantarkin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here