An shiga ruɗani a Kaduna bayan da ƴan sanda suka yi kokarin tarwatsa mambobin kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Islamic Movement Of Nigeria da ke karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky, wadanda ke gudanar da tattakin nuna goyon baya ga al’umma Falasdinu a tsakiyar birnin.
Bisa al’ada dai duk Juma’ar karshe ta watan Ramadan, ‘yan uwa Musulmi na gudanar da tattakin domin nuna wa al’ummar Falasdinu goyon baya dangane da irin “zaluncin” suka ce kasar Isra’ila na yi musu.
Mambobin kungiyar sun taru a kan shatale-talen Katsina da ke kan titin Ahmadu Bello Way kafin ‘yan sanda su yi kokarin tarwatsa su.
Hakan ya janyo fargaba tsakanin mazauna birnin ma wadanda suke da shaguna a kusa da hanyar.
An ruwaito cewa da dama daga ‘yan kasuwa sun rufe shagunansu domin gudun abin da zai faru.
‘Yan sanda a Kaduna sun ce tattakin mambobin ‘yan Shiar na yau yana a matsayin haramtacce.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ASP Mansir Hassan, ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa mambobin kungiyar sun fito da sanyin safiyar yau “rike da makamai, inda suka fara far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da sunan tattaki”.
Mansir ya ce “mambobin kungiyar sun far wa ‘yan sanda lokacin da suka yi kokarin tarwatsa su”, inda ya ce har ta kai wasu daga cikin jami’ansu sun jikkata.
Ya ce an kama wasu daga ciki da ake zargi da rike muggan makamai kuma za a gurfanar da su gaban kotu idan aka kammala bincike.
To sai dai mabiya Sheikh Zakzaky sun musanta inda suke cewa ‘yan sandan ne suka far musu da manufar hana su gudanar da tattakin nasu.
Wanan dai ba shi ne karo na farko ba da ‘yan Shia ke gudanar da muzahara duk da haramta musu hakan da gwamnatin tarayya ta yi karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.