Rundunar yan sandan Kano ta kama ƴan daba da sauran masu laifi 120 a wata guda

0
173

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama mutum 120 da ake zargi da yin daba da garkuwa da mutane da sauran laifuka cikin wata ɗaya a sassa daban-daban na jihar.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Asabar ɗin nan.

Ya ƙara da cewa an kama akasarin ƴan dabar ne a cikin birnin Kano musamman unguwar Dorayi daga ranar 1 zuwa 31 ga watan Maris da ya gabata.

Da yake yin bayani dalla-dalla kan rukunin masu aikata laifuka da jami’ansu suka kama, Kiyawa ya ce an cafke mutum 55 da ake zargi da yin daba, da masu garkuwa da mutane huɗu da masu safarar miyagun ƙwayoyi 10.

Ya ƙara da cewa an kama ƴan fashi da makami 15 da ɓarayin motoci huɗu da ɓarayin A-Daidaita-Sahu uku da ɓarayin babura bakwai da ƴan damfara biyu da ɓarayi gama-gari 20.

Kazalika Kiyawa ya ce sun kuɓutar da mutum uku daga hannun masu garkuwa da mutane tare da ƙwato tarin makamai a wurin masu aikata laifuka daban-daban.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu waɗannan nasarori ne sakamakon haɗin-kai da ta samu daga al’ummar gari, tana mai yin kira a gare su da su ci gaba da taimaka mata wurin tabbatar da tsaro a jihar, wadda ita ce mafi yawan jama’a a arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here