Tinubu zai tafi Legas don yin bikin sallah

0
139

Shugaba Bola Tinubu, zai bar Abuja babban birnin Najeriya ranar Lahadi zuwa Legas don yin bikin karamar sallah. 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Asabar. 

“Shugaba Tinubu zai yi bikin sallah ne tare da iyalansa a Legas, inda zai yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’a, musamman ganin irin tarin matsaloli da kasar ke fama da su,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here