Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta ce jimillar maniyyatan kasar dubu 50 ne ake sa ran zasu sauke farali a bana duk da karin kudin kujera da aka samu.
Shugaban hukumar Malam Jalal Arabi ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a birnin tarayyar kasar Abuja.
Jalal ya ce tuni aikace-aikace suka yi nisa a hukumar don tabbatar da gudanar da aikin hajjin na bana cikin nasara.
A cewar sa adadin mutanen da suka biya kujerar aikin hajjin na bana ya bada mamaki kwarai, idan aka yi duba da irin tsadar da kujerar tayi da kuma halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi.
Ya ce shirin aikin Hajjin bana, na cikin mafi wahala da hukumar ta gani sakamakon kalubalen da suka shafi kudi da ya zo da shi, lamarin da ya tilastawa hukumar kasa fara shiri akan lokaci.
Malam Arabi a kuma yabawa gwamnatin tarayya kan kokarin da ta yi na baiwa hukumar dukannin gudunmowar da take bukata, yana mai cewa ba don haka ba, zai yi wuya hukumar ta iya shirya aikin hajji a bana.
Bayanai sun ce kasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeru dubu 94 ne a bana, amma sakamakon matsin tattalin arziki da tsadar kujerar ya sanya sama da kujeru dubu 45 ke kasa har yanzu ba tare da an siya ba.