NDLEA ta cafke mai safarar hodar iblis a Legas

0
146

Jami’an Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani fasinja a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas ɗauke da kullin hodar iblis guda 80.

An kama Ogbonna ne a ranar Lahadi, 31 ga Maris, 2024, a lokacin da yake yunkurin hawa jirgin Qatar Airways zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya, ɗauke da fasfo ɗin ƙasar Laberiya. 

NDLEA ta bayyana kama mutumin ne a wata sanarwa da kakakinta Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi.

Babafemi ya ce an yi wa wanda ake zargin gwaje-gwaje, inda aka gano cewa yana tu’amalli da miyagun kwayoyi. 

“Mun yi mamaki da muka gano yawan kwayoyi da a haɗiye a cikinsa, nan da nan ya fara yin amai na kullin hodar iblis da ya haɗiye,” in ji Babafemi. 

NDLEA ta ce mutumin da ake zargi ya yi iƙirarin cewa wani dan uwansa ne ya ɗauke shi aiki don ya rika safarar kwayoyi.

An kuma samu ɗaurin hodar iblis guda 80 mai nauyin kilogram 889 a wajensa wanda ya amayar cikin kwanaki huɗu. 

“Abin da ya kusa janyo ya rasa rayuwarsa shi ne, Ogbonna ya ce an ba shi kwayoyi domin ya hadiye a wani otel a Ikeja, tare da yi masa alkawarin tukuicin Naira 300,000 idan ya yi nasarar kai hodar iblis din zuwa Indiya,” in ji sanarwar NDLEA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here