Za mu gabatar da kudurin kin amincewa da karin kudin wutar lantarki – Ndume

0
150

Babban mai tsawatarwar Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce ba wannan ne lokacin da ya dace a yi ƙarin kuɗin wutar lantarki ba ga ‘yan ƙasar.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Sanata Ndume ya ce wutar da babu ita ta yaya za a yi ƙarin kuɗi a kanta, ya shawarci gwamnati da ta fara samar da ita gabanin yin ƙarin kudinta.

“Babbar maganar ita ce kamfanonin da aka raba musu tashoshin bayar da wutar nan ba su biya kudaden ba ma tukunna har yau. Na biyu babu wutar, tun da aka ba su ba su habbaka yayyukansu ba.

“Gwamnati ta cefananr da wutar da zimmar ko za ta habbaka, amma kullum ƙara taɓarɓarewa take yi,” in ji Sanatan.

Ya ce da zarar majalisarsu ta koma hutu a ranar 16 ga watan Afrilu, shi da wasu abokan aikinsa za su jagoranci gabatar da ƙuduri kan janye wannan ƙarin.

Za kuma su bayyana cewa ya kamata duk abin da za a yi da ya shafi rayuwar talakawa ya ji ra’ayoyinsu gabanin aiwatar da shi, za kuma a iya cimma haka ne ta sauraren ra’ayinsu ‘yan majalisa a matsayin wakilan al’umma.

“Kamata ya yi idan za a ƙara kuɗin wuta a samar da ita, a ƙara albashin ma’aikata sannan a tabbatar da hauhawar farashin kayayyaki ya yi ƙasa”.

Ya kuma ce abin kunya ne raba wutar lantarki mataki daban-daban, akwai ta masu kuɗi akwai ta talakawa.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here