Bikin Sallah: Gwamnatin Kano ta baiwa fursunoni da shanu da kayan abinci

0
173
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya gwangwaje fursunoni da ke faɗin gidajen yarin jihar da shanu da kuma kayan abinci domin su samu damar gudanar da bukukuwan karamar Sallah cikin annashuwa.

Shugabar kwamitin yin afuwa ta jihar, Azumi Namadi Bebeji wadda ta wakilci gwamnan wajen raba kayan tallafin, ta faɗa wa fursunonin cewa su ma kamar sauran al’umma suke, kada su ɗauka an yi watsi da su. 

Bebeji ta tabbatar wa fursunonin cewa gwamnatin jihar ba za ta nuna gajiyawa ba wajen ci gaba da tallafa musu.

Ta yi kira ga fursunonin da su yi wa gwamnatin Abba Kabir addu’a domin ta ci gaba da samarwa jama’a ribar dimokraɗiyya.

Kwanturola na gidajen gyaran hali na jihar ta Kano, Salaiman M Inuwa ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, inda ya ce hukumar a shirye take wajen haɗa gwiwa da gwamnati a kodayaushe domin inganta tsarin yanke hukunci a jihar.

Ya ce tallafin da gwamnan ya bayar zai zaburar da fursunonin wajen bin doka da oda bayan sallamar su.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here