An samu bullar bakuwar cuta a Sokoto – NCDC

0
249

Hukumar Yaƙi Da Yaduwar Cututtuka Ta Najeriya NCDC ta tabbatar da ɓullar wata bakuwar cuta a Jihar Sokoto.

Babban daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ya ce kawo yanzu an gano mutane 164 da ake zargin sun kamu da cutar a yankuna shida na Karamar Hukumar Isa da ke jihar.

Yankunan sun haɗa Bargaja inda aka samu mutane 22 sun kamu, sai Isa ta Arewa mutum 17 sai Isa ta Kudu mutum 98 da mutum 12 a Tozai da wasu huɗu a Tsabre sai kuma Turba inda aka samu mutane 11.

Daraktan ya ce, “yawancin waɗanda cutar ta kama yara ne ’yan shekaru huɗu zuwa sha uku da kuma waɗansu manya.”

Dokta Jide ya ce, kawo yanzu sun tura jami’ai domin ɗaukar matakan gaggawa da zimmar dakile yaduwar cutar.

Ya ce, an taba samun makamanciyar irin wannan cutar a shekarar 2023 inda har ta wuce ba a san asalinta da maganinta ba.

“Yanzu haka akwai mutane biyu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Ɗan Fodio da ke Sokoto suna karɓar magani, kawo yanzu an sallami ɗaya daga cikinsu, ɗayan kuma yana ci-gaba da samun sauki.”

Ya ce, “Akwai wasu mutane hudu da ake zargin suna ɗauke da cutar a babban asibitin Isa, yayin da akwai kimanin mutane 130 da ke samun kulawa a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ko kuma a wasu wuraren karbar magani.”

Babban daraktan hukumar ta NCDC ya ce tantancewar farko na asibiti da kuma binciken al’amuran da aka shigar a asibitin koyarwa sun kawar da asalin cutar da aka samu, wanda hakan ya sa ake buƙatar neman wasu dalilai da suka haɗa da gwajin gano sinadarai na ƙarfe a jikin waɗanda cutar ta kama.

Ya buƙaci al’umma su yi taka tsantsan, su kuma kai rahoton duk wanda ya aka ga alamar cutar a tattare da shi zuwa cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa da su ko kuma a kira layin wayar NCDC kyauta.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here