Kotu ta amince  Zuma ya tsaya takarar shugaban kasar Afirka ta Kudu

0
150

Wata kotun Afirka ta Kudu ranar Talata ta amince tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ya tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Mayu.

Kotun ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗauka na haramta wa Mr Zuma tsayawa takara saboda samunsa da laifi a baya. 

Kotun ta ce Zuma, mai shekara 81, zai iya tsayawa takara duk da yake yana goyon bayan jam’iyyar hamayya ta Mkhonto we Sizwe (MK), wadda ake ganin za ta taka rawa a zaɓen.

“An yi watsi da matakin Hukumar Zaɓe,” in ji hukuncin da kotun ta yanke wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani.

Ba ta yi ƙarin bayani ba game da dalilan yanke hukuncin.

Ranar 29 ga watan Mayu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Afirka ta Kudu wanda masu sharhi ke gani zai kasance mafi zafi tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1994.

Damar da Zuma ya samu ta tsayawa takara za ta iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓen.

Ana sa rai jam’iyyar MK za ta samu tagomashi saboda goyon bayan da Zuma yake ba ta, kuma tana iya samun ƙuri’u a mahaifarsa waɗanda a baya jam’iyyar African National Congress (ANC) take buga ƙirji da su.

Hakan ka iya sanyawa ANC ta sha kashin da ba ta taɓa fuskanta ba a shekarun talatin da ta kwashe tana mulki, kuma tana iya rasa kaso 50 na ƙuri’un da ake buƙata don kafa majalisar dokoki.

Tun da farko hukumar zaɓen kasar ta haramta wa Zuma tsayawa takara, inda ta ce kundin tsarin mulkin ƙasar bai amince mutumin da aka yanke wa hukunci har ya yi zaman gidan yari na wata 12 tsayawa takara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here