Netanyahu yana tafka kurakurai a Gaza – Shugaban Amurka

0
165

Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce firaiministan isra’ila, Benjamin Netanyahu yana tafka kurakurai a hare-haren da Isra’ilar ke kai wa Gaza.

Da yake magana da sashen Sipaniyanci da ke kasar Amurka da ake kira Univision, Biden ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza da suka yi sanadiyyar mutuwar ‘yan agaji guda bakwai abun ‘tayar da ghankali ne, inda ya yi kira da a tsagaita wuta.

Hirar ta mista Biden wadda ke da tsawon awa guda an nade ta ne ranar Larabar da ta gabata kuma aka watsa ta ranar Talata da daddare.

Shugaban Amurka dai ya yi suna wajen mara wa Isra’ilar baya a yakin da take yi da a Gaza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here