Tsohon ministan Buhari, Ogbonnaya ya rasu

0
163

Tsohon ministan kimiyya da fasaha da kirkira na Najeriya, Chief Ogbonnaya Onu ya rasu yau Alhamis.

Marigayin maishekaru 72 wanda dan asalin jihar Ebonyi ne ya rasu bayan gajeruwar jinya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu wanda ya bayyana alhinin rashin maraigayin ya ce Chief Onu da mutumi dan kishin kasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hade kan Najeriya.

Chief Ogbonnaya Onu dai shi ne gwamnan farko na jihar Abia sannan ya kasance shohon shugaban jam’iyyar ANPP kuma jigo a kafa jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here