Wani almajiri ya fille wa dan shekara shida kai a Kano

0
210
Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan al’amarin da ya biyo bayan zargin fille kan wani karamin yaro ɗan shekara shida da wani almajiri ya yi a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi.

Rahotanni dai sun nuna cewa almajirin mai shekaru 22 ya kashe yaron ne a kusa da wata makarantar firamare kafin ya cire kansa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya shaida wa BBC cewa almajirin bayan ya yanke wa yaron kai ya jefa da kan a cikin wani masai.

“A jiya ne aka wayi gari da wannan labari da ke cewa wasu masu ruwa da tsaki suka lura da cewa sun ga wani yaro a wannan ƙauye da wuƙa wanda suka ga alamun jini a jikin wuƙar kamar jinin ɗan Adam ne, Hakan ne ya sa suka zarge abin da ya sa ‘yan unguwa suka cafke shi, suka tasa shi gaba, sai suka ga gangar jikin mutum inda ya amsa shi ne ya kashe shi.

Bayan da ƴan sanda suka je, shi ne ya ja su ya kai su inda ya wurgar da kan, inda suka ga kan yaron.” In ji kwamishinan ‘yan sanda na Kano.

Da BBC ta tambayi kwamishinan inda iyayen yaron da aka kashe suke, ya ce “Iyayen wannan yaron da aka kashe suna nan a cikin garin Kanwa kuma ba yadda za su yi face su rungumi ƙaddara kuma fatanmu shi ne muna yi musu ta’azziya kuma Allah ya ƙara musu hakuri.”

Ƙwamishinan ya ce almajin ya ya kashe yaron amma sai ya zama kamar kurma, ba ya amsa tambayoyin da ake yi masa ballantana su gano waɗanda ke da alaƙa da laifin da ya aikata.

“Lokacin da aka kama almajirin da cewa asirinsa ya tonu, ba ya iya magana ko kuma ba ya iya kammala magana saboda dukan da aka yi masa kafin zuwan ƴan sanda.

Allah ya sa a lokacin da ƴanda suka je wurin, ba a riga an kashe yaron ba, sai muka kai shi asibiti, inda likitoci suka fara aikin ceton ransa sakamakon haka ya sa ba mu iya ƙarasa masa tamboyoyi ba daga bisani kuma sai rai yayi halinsa.” in ji kwamishinan.

Kwamishinan ya ƙara da cewa damuwar ƴan sanda jihar Kano shi ne ɗaukar doka a hannu da mutane ke yi wanda hakan ke hana su samun bayanan da ya dace kuma da suke buƙata wajen binciken laifuka.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here