Hezbollah ta yiwa arewacin Isra’ila lugudan wuta

0
223

Rahotonni na bayyana cewa mayakan Hezbollah na harba bama-bamai ta sama zuwa arewacin Isra’ila.

An harba rokoki da dama daga kudancin Lebanon zuwa arewacin Isra’ila da kuma yankin Golan da ta mamaye.

Ana iya jin karar makamai masu linzami da ke karo da makaman roka a yankin kan iyaka da ke kudancin Lebanon.

Har ila yau kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ta harba makamai masu linzami ga makiyanta a Zaoura da kuma rokokin Katyusha da dama domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani ga hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a kudancin Lebanon.

Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa, makamai masu linzami 40 aka harba mata daga yankin Lebanon, amma an samu nasarar lalata wasu daga cikinsu kafin su sauka.

Sai dai kungiyar ta masu tsatssauran ra’ayi ta tabbatar da cewa, makamai masu linzami guda 50 ta harbawa Isra’ilan.

An kashe bayahude mutum daya a wurin da ‘yan kama wuri zauna ba bisa ka’ida suka mamaye a garin al-Mughayyir da ke gabar yammacin kogin Jorda.

Wannan dai na daya daga cikin hare-haren ‘yan tawaye kusan 700 tun ranar 7 ga Oktoba da Isra’ila ta fuskanta.

A Gaza sojojin Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat yayin da a yammacin gabar kogin Jordan, wani samame da aka kai a gundumar Tubas ya kashe Falasdinawa akalla biyu.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here