Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila

0
194

Iran ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila ta hanyar amfani makaman roka da kuma jirage marasa matuka.

Wata sanarwa daga Dakarun juyin-juya-hali na kasar Iran (IRGC) ta ce “an harba gwamman jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami zuwa cikin yankin kasar Isra’ila.

Dama an shiga fargaba kan yiwuwar barkewar fada tsakanin Iran da Isra’ila tun bayan zargin da Isra’ilar da kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria ranar daya ga watan Afrilu.

Harin ya yi sanadiyyar kashe jami’an Dakarun juyin-juya-hali na Iran, wadanda suka hada da janar-janar guda biyu da kuma wasu ‘yan kasar Syria shida.

Tun a wancan lokaci ne Iran ta yi gargadin cewa ‘Isra’ila za ta dandana kudarta’.

Sanarwar da Iran ta fitar ta kara da cewa harin na yammacin ranar Asabar martani ne kan “manyan laifukan da Isra’ila ta sha tafkawa” – ciki har da harin ranar daya ga watan Afrilu.

Bayanin ya ce an yi wa wannan hare-hare da Iran ta kaddamar taken “Operation True Promise” a turance.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan yanayin harin ba, baya ga cewa kasar ta harba gwamman makamai zuwa cikin Isra’ila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here