Wadanda suka dakatar da Ganduje ba ƴan APC ba ne – Abdullahi Abbas

0
151
Ganduje
Ganduje

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce za ta ɗauki mataki kan ɓangaren da ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Litinin ne wani reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar ta kasa, daga bisani kuma shugaban jam’iyyar APC din a matakin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya yi watsi da matakin.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Abdullahi Abbas ya yi zargin cewa waɗanda suka dakatar da Ganduje makusanta ne ga wasu masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar da NNPP ke mulki.

Ya shaida cewa sun duba jerin sunayen ƴan jam’iyyar na mazaɓar Ganduje, “mutum 27 ne kowace mazaɓa, mun duba a cikin su gaba ɗaya babu ko ɗaya da yake a cikin shugabanni.”

A cewarsa, jami’in da aka ce ya sanar da dakatar da Gandujen, Haladu Gwanjo, ya ce zai je kotu ya nemi haƙƙinsa saboda an zalunce shi.

Abdullahi Abbas ya bayyana cewa “wannan ba abin da ya haɗa shi da jam’iyyarmu, wannan tsari ne na gwamnatin jihar Kano da jam’iyyarsu ta kayan gwari suka shirya, ina tunanin wannan [ita ce] hanyar da za su ci mutuncin dakta Ganduje.”

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here