Kotu ta hana EFCC kama Yahaya Bello

0
166

Wata babbar kotun jihar Kogi ta hana hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello

Mai Shari’a I.A Jamil ne ya bayar da umarnin yayin zaman da kotun ta yi a yau Laraba, inda ta ba da umarnin hana tsarewa da kuma tuhumar tsohon gwamnan. 

Alƙalin ya ce yunƙurin tauye wa Yahaya Bello haƙƙi “haramtacce ne” har sai kotun ta ba da umarnin yin hakan, kamar yadda kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito. 

Sai dai jami’an hukumar na can sun yi wa gidan tsohon gwamnan ƙawanya a unguwar Zone 4 da ke Abuja babban birnin ƙasar domin kama shi. 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan Kogi na yanzu, Usman Ododo, ya ziyarci Yahaya Bello a gidan kuma akwai yiwuwar shi ne ya fitar da shi daga gidan a motarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here