Ƙungiyar ƴan canji ta Najeriya ta ce ƴan canji sun fara sayan dala ɗaya a kan naira 980 a kasuwar bayan fage sannan su sayar kan naira 1,020.
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Aminu Gwadabe ne ya tabbatar da haka a hirarsa da gidan talabijin na Channels inda ya ambaci cewa darajar naira ta ƙaru a lokaci kaɗan da ba a taɓa tsammani ba.
Gwadabe ya jinjinawa gwamnati da kuma babban bankin ƙasar kan ƙoƙarinsu inda ya ce wannan ne karon farko cikin shekara 15 da farashin dala a kasuwar ƴan chanji ke ƙasa da farashin da ake saidawa a hukumance.
Ya shaida cewa yanzu babu raɗe-raɗin da ake yawan yi da ke zuzuta farashin dala.
Gwadabe ya ƙara da cewa “a halin yanzu muna siya daga gwamnati a kan naira 980 sannan mu sayar a kan naira 1,020”.
Masha Allah. Allah ya ingata mana tattalin arzikin kasan nan.