Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ja kunnen dan El-Rufai

0
193
Bello El rufai

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ce ba za ta lamunci kalaman ”rashin ɗa’a” daga wajen Bello El-Rufai, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa ba, a kan dambarwar da ake yi da ta shafi binciken gwamnatin mahaifinsa, tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

A sanarwar da majalisar ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, ta ce tun bayan da ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai binciki al’amuran da suka shafi kashe kuɗaɗe da karɓar basussuka daga shekarar 2015 zuwa 2023 a Jihar Kaduna, “sai Bello ya wallafa wasu kalamai a X na neman faɗa.”

Sai dai sanarwar mai ɗauke da sa hannun Suraj Bamalli, mai taimaka wa Shugaban Majalisar kan harkokin sadarwa, ta ce duk da cewa tuni Bello, ya goge saƙonnin, sun kasance “na raini ga kafatanin ɓangaren dokoki na jihar.”

Majalisar ta ci gaba da cewa “Jim kaɗan bayan kafa kwamitin da zai binciki harkokin kuɗi da rance da tallafi, da aiwatar da ayyuka daga 2015-2023 a jihar Kaduna, Hon. Bello Elrufai ya wallafa saƙonni biyu a shafinsa na Tuwita, waɗanda yanzu an goge su, yana mai kira da a yi faɗa…

“…da kuma rashin mutunta dukkan Bangaren Majalisar Dokoki. Bugu da ƙari, ya aike da saƙonnin ɓatanci ga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Liman ta WhatsApp,” in ji sanarwar.

Majalisar ta ce tuni saƙonnin suka watsu kamar wutar daji, inda suka jawo damuwa a tsakanin al’ummar Jihar kaduna.

“Abin takaici ne yadda ɗan Majalisar Tarayya, wanda aka bai wa wakilcin jama’a, zai nuna irin wannan hali, da yunƙurin kawo cikas ga dokokin Majalisar Jiha. Majalisar dokokin jihar Kaduna tana son tabbatar wa al’ummar jihar Kaduna nagari cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yin hidima ba tare da tsoro ko son rai ba,” a cewar sanarwar.

TRT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here