An saki sarkin da ya mika kansa kan zargin kisan sojoji 17 a Delta

0
153

Hukumomin sojin Najeriya sun saki Sarkin da aka ayyana nemansa ruwa a jallo bisa zargin hannu kisan dakarun soji 17 a Okuama da ke Ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Aminiya ta ruwaito yadda rundunar soji ta ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargi da aikata munanan aika-aikar da ta sa mazauna garin Okuama suka fice daga cikin unguwannin garin.

Jim kaɗan bayan samamen da jami’an suka kai, sojoji sun bayyana sunayen: Arthur Ekpekpo, farfesa; Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbono (wanda aka fi sani da Amagbem); da Akata Malawa David, waɗanda ake nema ruwa a jallo.

Sauran mutanen da aka bayyana sunayensu sun haÉ—a da: Sinclear Oliki, da Clement Ikolo Ogenerukevwe da Reuben Baru, da Igoli Ebi, mace É—aya tilo a cikin waÉ—anda ake nema ruwa a jallo.

Bayan sanarwar sojojin, Sarkin wanda lamarin ya faru a yankinsa mai suna Clement Ikolo Ogenerukevw ya miƙa kansa ga ‘yan sanda, inda su kuma suka miƙa shi ga sojoji.

Yayin da yake miƙa shi ga Sanata mai wakiltar Delta ta tsakiya a hedikwatar rundunar a ranar Juma’a, Nwachukwu ya ce Sanatan ya shaida halin kirki na sarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here