ECOWAS ta ba da gudumawar dala miliyan 9 ga yan gudun hijira a Najeriya

0
144

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta ce ta bada dala miliyan 9 don gudanar da ayyukan jin kai a yankin, a cikin wannan shekara.

A cikin sanarwar da kwamishinar da ke kula da ayyukan jin kai na ƙungiyar Farfesa Fatou Sow Sarr ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ƙungiyar ta fitar da kuɗin ne don kula da ƴan gudun hijira da masu neman mafaka hadi da garuruwan da suka karbesu a fadin ƙasahe 15 da ke ƙarkashin ƙungiyar.

Farfesa Fatou ta ce daga cikin kudin Najeriya ta samu dala miliyan daya da za a gudanar da ayyukan kula da ‘yan gudun hijirar da ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa da kula da wadanda suka samu raunuka sanadiyar hare-haren ‘yan ta’adda da dai sauransu.

Kwamishinar ta ce daga cikin dala miliyan 25 da aka ware don yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Najeriya da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, ECOWAS ta ware dala miliyan 4 don gudanar da ayyukan jin kai.

Farfesa Fatou Sow Sarr ta kuma ce ƙungiyar ECOWAS na maida hankali a kan matakan kariya, inda ta ce ƙungiyar na da tsarin rage fuskantar barazanar bala’oi da ya bada damar sanya ido kan yankunan da aka ɗai-ɗaita ko suka fuskanci ambaliyar ruwa.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here