Amurka za ta aike da tallafin soji zuwa Ukraine cikin mako guda

0
177
Joe Biden

Jami’an Amurka sun ce ƙunshin taimakon soji zai isa Ukraine cikin mako guda mai zuwa, bayan majalisar wakilai ta amince da tallafin dala biliyan sittin wanda ya haɗa da harsasai a ranar Asabar bayan shafe watanni ana kai ruwa rana.

‘Yan jam’iyyar Democrat da masu matsakaicin ra’ayi daga jam’iyyar Republican sun yi haɗin gwiwar wucin gadi don ganin ba a samu koma baya ba a taimakon da Ukraine take buƙata.

Kakakin jam’iyyar Republican, Mike Johnson ya raba gari da masu sukar ƙudirin a jam’iyyarsa don tabbatar da dokar.

Shugaba Joe Biden ya ce zai rattaɓa hannu kan buƙatar nan take, da zarar hakan ta faru kuma za a fara aika wa Ukraine da taimakon sojoji cikin gaggawa.

Shugaban na Amurka ya ƙara da cewar ƙuri’ar ta aike da saƙo ƙarara game da shugabancin Amurka a fagen duniya.

Mista Biden ya kuma buƙaci majalisar dattawan Amurka – wadda ake sa ran za ta amince da ƙudirin – ta gaggauta aike masa da shi domin ya saka hannu ya zama doka don gaggauta aika makamai zuwa Ukraine.

Sakatare janar na ƙungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana farin cikinsa game da zartar da ƙudirin wanda ya ce ya tabbatar da haɗin kan ƙasashen ƙungiyar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here