Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan Lahadin a Jamhuriyar Nijar, don neman sojojin Amurka su gaggauta ficewa daga ƙasar da ke karkashin mulkin soja, dai dai lokacin ake ɗakon wata tawaga daga Washington cikin ‘yan kwanaki masu zuwa domin shirya janyewar sojojin cikin tsari.
Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula 24 da ke goyon bayan gwamnatin ƙasar tun bayan juyin mulkin bara ne suka kira zanga-zangar da aka yi a garin Agadez da ke arewacin Hamada, inda sansanin sojin Amurkan mafi girma a Afirka ya ke.
A ranar Juma’a ne Amurka ta amince da janye sojojinta fiye da 1,000 daga ƙasar ta Afirka inda Washington ta gina wani sansani da ta kashe dala miliyan 100 domin sarrafa jiragen yaki marasa matuka.
Masu zanga-zanagar na rike da allunan da ke dauke da sakonnin bukatar ficewar dakarun Amurka.
“Nan Agadez ne, ba Washington ba, sojojin Amurka za su koma gida”