Gwamnatin Sokoto ta tube Uwayen Kasa 15 daga kujerunsu

0
212
Ahmad Aliyu

Gwamnatin jihar Sokoto ta tube wasu Uwayen kasa 15 daga mukamansu.

Daga cikinsu kuma akwai shida da gwamnatin ta tube wadanda tsohuwar gwamnatin PDP ta nada.

Gwamnatin ta kuma sanar da mayar da wasu uwayen kasar da ta dakatar daga aiki kan kujerunsu.

Daga cikin wadanda ta tube su 15 akwai 9 da ta ce an tube su ne bayan zarginsu da hannu a matsalar tsaron jihar da kuma wawurar filaye da nuna rashin biyayya

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin tube uwayen kasar ne bisa sakamako binciken da kwamitin da ta kafa ya gano kuma ta yi aiki da shawarwarin kwamitin.

Gwamnatin ta kuma mayar da wasu uwayen kasa da aka dakatar kan kujerunsu, kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Honarabul Bello Sambo Danchadi ya shaida wa BBC.

Ya ce akwai uwayen ƙasa da aka kuma sauya wa wuri, sai wadanda aka sauke sun hada da na Unguwar lalle da Yabo da Wamakko da Tilluwa da Illela da Dogon Daji da sauransu wanda gwamnatin ta ce an same su da laifin rashin biyayyah da kuma ƙin bayar da hadin kai ga yaƙin da take da rashin tsaro.

Gwamantin jihar Sokoton ta ce ta kuma soke wasu naÉ—e-naÉ—e da gwamnatin da ta gabata ta yi bayan ta faÉ—i zaÉ“e, wanda gwmanatin mai-ci ke ganin an yi haka ne da gayya,”Akwai Marafan Tangaza da Sarkin Gabas Kalanbaina da kuma Sarkin Kudun Yar tsakuwa, Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Toronkawa.”

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne bayan da kwamitin bincike ya gabatar da bincike, inda ta ce babu batun siyasa a ciki.

Sai dai tsohuwar gwamnatin Aminu waziri tambuwar ta mayar da martani kan matakin musamman tube sarakunan da ta nada, matakin da ta danganta da siyasa.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP a jihar sokoto Hassan Sahabi Sanyinnawal ya ce matakin bai ba su mamaki ba “Sarakunan da aka ce an dakatar saboda ba a bi Æ™a’ida wajen nadasu ba, na yi mamakin yadda gwamnati za ta ce ba a bi Æ™a’ida ba, domin Æ™a’ida ita ce mutum ya gaji sarauta kuma an bi dukkan matakan da doka ta tanada wajen nadasu.”

Hassan Sanyinna ya ce lokacin da tsohon gwamnan Aminu Waziri ya yi naÉ—i doka ta ba shi dama ya nada duk wanda zai nada a matsayin sarki.

Baya ga tube sarakunan da mayar da wasu kan kuejrunsu, gwamnatin ta kuma ce akwai wasu wadanda take gudanar da bincike a kansu, ba tare da sanar da tsawon lokacin da binciken zai dauka ba.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here