Hajji: Saudiyya ta gargadi maniyyata game da kamfanonin bogi

0
143
Hajji

Ma’aikatar aikin Hajji da Umara ta yi gargadi ga maniyyta aikin hajjin bana da su lura da su lura da kamfanonin bogi da ke tallata kansu a kafafen sada zumunta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar ta ce ya kamata maniyyata su sani cewa ana samun bizar aikin Hajji ne kawai ta hannun hukumomin Saudiyya ko kuma hanyoyin da hukuma ta san da zamansu.

Ma’aikatar ta yaba wa hukumomin majalisar IraÆ™i na aikin da suka yi tare domin tabbatar da an kama wasu kamfanonin bogi 25 da suke aiki.

Irin kuma wannan haÉ—in kan Ma’aikatar ke fatan ganin an cimma da sauran kamfanonin Æ™asashen duniya domin kama wandanda ba su da izinin gudanar da ayyukan Hajji da Umra.Ta kuma shawarci al’umma su zama ma su sanya idanu tare da shigar da rahoton duk wani kamfanin da suke zargi da ke tallan kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here