Mun zuba jari a bangaren fasaha domin yaki da cin hanci – Tinubu

0
140

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na zuba jari matuƙa a ɓangaren fasaha wadda za ta taimaka wurin kawo ci gaba ga gwamnatin Nijeriya. 

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da shugaban kamfanin Microsoft wato Bill Gates, bayan sun haɗu a birnin Riyadh na Saudiyya a ranar Lahadi. 

Shugaban ya bayyana cewa fasaha ta kasance wani makami da ake amfani da shi domin yaƙar cin hanci da rashawa da kuma yaƙar yadda ake wadaƙa da kuɗaɗen al’umma. 

Tinubu ya jaddada cewa ana samun turjiya daga wurin al’umma a yunƙurin da ake yi na amfani da fasaha wurin kawo ci gaba. 

“Fasaha abokiyar gaba ce ga cin hanci da aikata ba daidai ba. Muna ta aiki tuƙuru domin inganta fasaha,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban ya bayyana cewa lokacin da yake gwamnan Legas, ya yi amfani da fasaha domin tattara bayanai da kuma amfani da su wurin karɓar haraji, wanda hakan ya samar da tsari mai kyau na karɓar haraji. 

A martanin da ya mayar, Mista Gates ya shaida wa shugaban ƙasar kan cewa akwai wata manhaja ɗaya wadda za a iya amfani da ita wurin haɗe bayanai da suka shafi tsare-tsare da tsaro da kuma kula da haraji. 

“Muna aiki tare da Mista Wale Edun, wanda shi ne Ministan Tattalin Arziki da Kuɗi kan batun fasahar zamani. Kafin ka karɓi mulki, akwai wasu abubuwa kaɗan da aka yi ƙoƙarin haɓaka manhajar tattara bayanai. Sai dai an bar su sun warwatsu. Akwai manhajoji da dama na tantance bayanan mutane. 

“A yanzu akwai shirin da ake yi na amfani da fasahar nan ta MOSIP wurin tattara bayanai ta yadda jama’a za su iya samun abubuwansu ta yanar gizo. Za mu iya taimakawa ta wannan ɓangaren kuma za mu iya bayar da ƙarin taimako,” in ji Bill Gates.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here