Tsananin zafi: Mahukunta sun gargaɗi al’umma kan yaduwar cututtuka

0
110
Tsananin zafi

Mahukunta sun gargaɗi Kanawa dangane da ɗaukar duk wasu matakai da suka dace domin kaucewa kamuwa da cututtuka sanadiyyar tsananin zafin rana da ake fama da shi.

Hukumar kula da asibitocin Kano ce ta shawarci al’ummar jihar da su gaggauta ziyartar asibiti mafi kusa da su da zarar sun ji wasu alamu na rashin lafiya a jikinsu.

Sakataren hukumar, Dokta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman ta sanya wa hannu.

Dokta Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da shawarar ne don kauce wa cutar ƙyanda, sanƙarau da duk wata cuta da ake samu sakamakon tsananin zafi da jihar ke fuskanta.

Sanarwar ta ce alamomin cututtukan sun haɗa da zazzaɓi mai tsanani da ciwon kai da amai da ciwon wuya da bushewar maƙogoro da kasala da sauran alkamomi.

Dokta Mansur Mudi Nagoda ya ce za a samar da tawagar gaggawa ta musamman da za ta riƙa kula da marasa lafiya a asibitocin jihar.

Sanarwar ta kuma ce mutanen da ke fama da ciwon siga da hawan jini su nemi shawarar likitoci a wannan lokaci da ake fama da tsananin zafi.

Shugaban hukumar ya kuma shawarci mutane su yawaita shan ruwa tare da guje wa yawo a cikin rana, da kauce wa kwanciya a ɗakunan da ke cike da cunkoso.

Jihar Kano da wasu yankunan Arewacin Najeriya na fama da tsananin zafi, lamarin da ake fargabar ɓarkewar cutukan da ke da alaƙa da zafin.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here