Karancin mai: Majalisa ta gayyaci ministan mai gabanta 

0
165

Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci ministan albarkatun mai saboda matsalar karancin man da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a sassan ƙasar.

Shugaba Bola Tinubu ne ministan albarkatun mai yayin da Heineken Lokpobiri ne ƙaramin ministan albarkatun mai.

Ƴan majalisar dai ba su fayyace wanda suka gayyata ba duk da cewa ba lalle bane su gayyaci shugaban ƙasar.

Matakin gayyatar ministan ya zo ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa Shehu Ajilo daga jihar Kaduna ya gabatar bayan dawowar majalisar bakin aiki bayan hutun kwana 40.

Ministan zai yi wa ƴan majalisar bayani game da matsalar ƙarancin mai a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here