Mun kama mutumin da ya kitsa harin jirgin kasa na Kaduna – ‘Yan sanda

0
177

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutumin da ya kitsa hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna, inda aka yi garkuwa da mutane da dama a watan Maris na 2022. 

A cewar rundunar, an kama Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da Mande bayan tattara bayanan sirri a yankin Æ™aramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. 

Haka nan, mai magana da yawun rundunar ‘yans sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, Mande da sauran tawagarsa ne suka sace É—aliban Jami’ar Greenfield. 

“A ranar 12 ga watan Janairun 2024, dakarun yaÆ™i da garkuwa da mutane na Kaduna suka yi wuf tare da kama Mande a kusa da gadar sama ta Rido da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna,” a ACP Olumuyiwa Adejobi.

A ranar Alhamis ne rundunar ta gabatar da Mande tare da wasu mutum 30, waÉ—anda ta ce “sun sha addabar” mazauna yankunan da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ta hanyar sacewa da kuma kashe matafiya. 

“Ana kallon Mande a matsayin jagoran ‘yanfashi kamar Bello Turji, da Dogo Gide,” in ji kakakin ‘yansandan. 

Wannan ne karon farko da jami’an tsaro suka ce sun kama wani da zargin hannu a kai hari kan jirgin Æ™asan, wanda gwamnatin Najeriya ta zargi Æ™ungiyar Boko Haram da kaiwa. 

Majiyoyi daga asibitin 44 na jihar Kaduna da aka kai wasu daga cikin mutanen da harin da ‘yan bindigar suka kai kan jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun ce mutum bakwai ne suka mutu.

Kazalika sun ce mutum ashirin da biyu suka jikkata, cikinsu har da tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Wakkala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here