An rage wa ‘yan rukunin ‘Band A’ farashin wutar lantarki 

1
156

Hukumar kula da samar da lantarki ta Najeriya ta rage farashin wutar lantarki ga waɗanda suka faɗa cikin rukunan ‘Band A’ masu samun ƙarfin wuta fiye da kowa a ƙasar.

Da yake tattaunawa da BBC, jam’in hukumar ta NERC, Usman Abba, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda karyewar darajar dala, inda yanzu farashin ya sauko daga naira 225/kWh zuwa naira 206.80.

“Daga cikin abubuwan da ake dubawa wajen ƙayyade farashin wuta akwai farashin kuɗaɗen ƙasar waje,” in ji shi. “Tun da an samu saukar dala to dole ne farashin mai ma ya sauko.” 

Najeriya na samar da lantarki ne ta hanyar amfani da tashoshi masu amfani da ruwa, da man fetur, da kuma iskar gas. 

A makwannin da suka gabata ne hukumar ta ƙara farashin lantarki ga al’ummar ƙasar waɗanda ke samun lantarki na fiye da awa 20 a kowace rana.

Lamarin ya haifar da koke-koke a faɗin ƙasar, inda masana ke fargabar hakan zai iya jawo ƙarin hauhawar farashi.

1 COMMENT

  1. Bayan rage farashin wutar ya kamata kuma duk wani rukunin unguwa dake amfani da mita a gidajensu ya kasance suna samun wutar lantarki na sama da a wanni 15 a rana

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here