Yan ta’adda sun tashi kauyuka 10 a Kaduna

0
176
Kaduna

Mazauna wasu kauyuka 10 a Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu saboda harin ’yan ta’adda masu satar mutane. 

Da dama daga cikin mutanen yankin sun tako da ƙafa ne domin samun mafaka a garin Giwa, hedikwatar karamar hukumar.

Wakilinmu Muhammad Ibrahim Yaba ya bayyana mana cewa an ga yara kanana da mata cikin yanayi na firgici suna ta tuttudowa cikin garin Giwa domin tsira da rayukansu.

Wakilin mazaɓar Giwa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Umar Auwal Bijimi, ya shaida mana cewa, an fara gudun hijirar ne tun bayan canza wa wani soja mai ƙwazo kuma kwararre mai suna Sajan Usman Hamisu Bagobiri wurin aiki.

Ya ce Sajan Bagorbiri ya taka muhimmiyar rawa wurin yakar ’yan fashin dake addabar yankin.

Dan majalisar ya ce, rashin Sajan Bagobiri ya bai wa ’yan ta’addar kwarin guiwa, lamarin da ya sa suke ta kai munanan hare-hare a kauyukan.

Honarabul Bijimi ya ce, kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Gogi da Unguwar Bako da Marge da Tunburku sai  Bataro da Kayawa da kuma Yuna.

Bijimi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin soji da su dawo da Sajan Bagobiri yankin, su kuma tura karin sojoji domin ci gaba da yakar ’yan bindigar.

Dagacin Fatika, Nuhu Lawal Abdullahi ya roki gwamnati da ta dauki kwararan matakai a kan ’yan bindigar da suka hanasu zaman lafiya a yankinsu.

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce masu ruwa da tsaki da suka haɗa da shugaban karamar hukumar Giwa, Abubakar Shehu Giwa, da masu sarautun gargajiya na tattaunawa da ma’aikatarsa dangane da matsalar tsaro a yankin.

Ya tabbatar da cewa labarin lamarin ya kai ga hukumomin da suka dace, kuma ana ci gaba da gudanar da shiri na hadin gwiwa domin inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da kuma ƙarfafa matakan tsaro a cikin yankunan da abin ya shafa.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here