Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu a dokar da za ta wajabta yin gwaji kafin aure, abin da ke nufin cewa dole ne daga yanzu duk wadanda ke shirin yin aure su yi gwaji.
Wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar ta Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce ya zama wajibi a yi wannan doka, don rage yawan yaran da ake haifa da matsalolin rashin lafiya kamar cutar sikila, HIV da cutar hanta ta hepatitis.
Sanrwar ta ce wanna mataki ya yi daidai da ƙudirin gwamnan jihar Kano na inganta, tareda samar da yanayi ia armashi a ɓangaren kiwon lafiya, da zummar rage ƙlubalen lafiya a jihar.
Dokar ta wajabta gwaji na cutar HIV, Hepatitis da rukunin jini na genotype, kafin aure. Dokar ta kuma haramta wariya ko kuma tsangwamar da ake wa masu rayuwa da cutar HIV, sikila, da sauran matsaloli na rashin lafiya.